Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta ce ta kama wata mota dankare da kayan zabe za a kai su Sokoto daga Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanda Celestine Okoye ya bayana wa manema labarai haka a garin Gusau.

Okoye, ya ce bincike ya nuna cewa, wasu ne da ba su da izinin daukar kayan zabe ne su ka dauki kayan domin kai su jihar Sokoto.

Ya ce Ma’aikatan su sun tare direban motar a wani shingen duba motoci, inda daga nan yayi kokarin arcewa har ya afka wa wasu masu tuka keke NAPEP biyu.

Okoye ya cigaba da cewa, tuni rundunar ta kama motar da direban, kuma ta na kan gudanar da bincike a kai.