Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi alkawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan dakarun sojin Nijeriya 16 a Jihar Delta.

Manyan jami’an soji hudu da kananan sojoji 12 a ka kashe a lokacin da su ke kokarin sasanta rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli a jihar.

Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin kasa sun samu amincewa ta hukunta duk wanda a ka samu da hannu a mummunan aikin da a ka yi kan al’ummar Nijeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan labarin yadda wasu sojoji su ka cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna yankin suka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.

A nashi bangaren, mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da harin kan yankin na Okuama, sai dai ya jaddada cewa dole ne sojoji su kwato makaman da a ka sace daga hannun sojojin da a ka kashe.

Leave a Reply