Masu fashin baki da masana fannin tsaro a Nijeriya, sun yi nazari a kan kalaman Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce duk wanda aka kama ya saci akwatin zabe ya yi a bakin ran sa.
Bayan wannan furuci na shugaba Buhari, tuni har wasu jami’an tsaro sun ce a shirye su ke su harbe duk wanda su ka kama, yayin da wasu ke ganin ai kalaman ba su saba wa kundin tsarin mulki ba.
Furucin na Shugaba Buhari dai ya haddasa muhawara mai tsanani a tsakanin kwararru a fanin tsaro da masana kundin tsarin mulkin kasa.
Wani kwararre a fannin kundin tsarin mulki Barista Yusha’u Waziri Mamman, ya ce Sashe na 31 da na 32 na kundin tsarin mulki, sun ba Shugaba Buhari hurumin daukar kowane mataki domin tsaron kasa, kuma banbancin abin da dokar zabe ta ce shi ne in an kama mai laifi a hukunta shi da sauri har na tsawon shekaru uku.
Shugaban kamfani tsaro na Bicon Sikuriti Kabiru Adamu, ya ce tun asali ana yi wa shugaba Buhari Kallon mai aiki da karfin soji, inda tuni har rundunan sojoji ta Fatakwal ta ce a shirye su ke su bi wanan umurni ka’in da na’in.