Dakta Mustapha Lecky, Kwamishinan Hukumar Na Kasa
Dakta Mustapha Lecky, Kwamishinan Hukumar Na Kasa

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta bayyana kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da zabubbukan kasar da za a yi ranar Asabar mai zuwa.

 Yayin da ya ke yi wa tawagar jami’an sa ido na ciki da wajen Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki jawabi, kwamishinan hukumar na kasa Dakta Mustapha Lecky da ya wakilci Farfesa Mahmaood Yakubu, ya ce Allah ne kawai ke da ikon dakatar da zabubbukan da aka shirya gudanarwa.

Ya ce a halin yanzu babu wani dalili da zai hana hukumar gudanar da zabubbukan kamar yadda aka tsara, duba da kwararan matakan da su ka dauka na tabbatar da komai ya tafi dai dai.

Hukumar zaben. ta kuma jaddada matsayin ta na fatan gudanar da zabe mafi tsafta a tarihin Nijeriya.

Ministan harkokin waje Geoffery Onyema, ya bukaci kasashen duniya su mutunta ‘yancin Nijeriya, su kuma kauce wa yi mata katsalandan a harkokin ta na cikin gida, inda ya yi gargadin cewa Nijeriya ba za ta yarda da kutse a cikin al’amuran ta ba bisa ka’ida ba.