Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce za ta biya kudin ladar aikin zabe naira dubu 30 da 500 ga duk masu bautar kasar da su ka shiga aikin zabe.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi dangane da shirye-shiryen da aka samu wajen gudanar da zabe a ranar Asabar mai zuwa.
Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce za a biya kowane dan bautar kasa naira dubu 30 da 500 a matsayin ladar aikin sa.
Wannan bayani kuwa ya zo ne kwana daya bayan wasu masu bautar kasa da za su yi akin zabe sun rika yada labarin cewa hukumar zaben ta fara kudin alawus, amma yadda aka biya wasu ya sha bamban da abin da aka biya wasu.
Rahotanni sun ce a ranar Juma’ar da ta gabata, da dama daga cikin ma’aikatan sun kai kan su wuraren da za su yi aiki ne, bayan hukumar ta yi jinkirin biyan su kudaden alawus na horo har naira 4,500 da aka yi masu alkawari.
Wannan ya sa masu bautar kasa su ka rika yada barazanar cewa idan ba a biya su kudaden ba lallai ba za su yi aikin zaben ba.