Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Na Kasa
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Na Kasa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce ta kammala aikin sake saita na’urar tantance masu kada kuri’a.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai da ya yi bayan dage zaben da aka yi a makon da ya gabata, inda ya ce an samu nasarar saita na’urorin gaba daya.

Farfesa Mahmud, ya ce ya na farin cikin shaida wa jama’a cewa an cimma nasarar sake saita na’urorin tantance masu kada kuri’a baki daya.

Ya ce kowace na’ura an saita ta ne da rumfar zaben da za ta yi aiki da ita, kuma ba zai yiwu a iya bude ta har a yi aiki da ita ba sai zuwa ranar Asabar daga karfe 8 na rana, a wani mataki na guje wa magudi kafin zabe.