Gwamnatin kasar Amurka, ta rufe ofisoshin jakadancin ta da ke jihar Legas da na birnin tarayya Abuja, biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi cewa babu aiki a ranar Juma’a, 22 ga watan Febrairu.

Amurka ta bayyana haka ne a ciki wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce ta rufe ofisoshin ne domin ba ‘yan Nijeriya da ke aiki a ofisoshin damar shirin kada kuri’un su a zaben da za a yi ranar Asabar din nan.

Don haka ta  shawarci duk abokan huldar ta da ke son zuwa daya daga cikin ofishin ta a ranar Juma’a su dakata har sai bayan zabe.

Idan dai za a iya tunawa, tun ranar Larabar da ta gabata ne, gwamnatin tarayya ta sanar da Juma’a a matsayin ranar hutu domin a ba ‘yan kasa damar shirya wa zaben ranar Asabar, sai dai sanarwa ta cire bankuna da ma’aikatan su daga cikin wadanda za su yi hutun.