Sanata Rafiu Ibrahim, Mai Wakiltar Mazabar Kudu Jihar Kwara
Sanata Rafiu Ibrahim, Mai Wakiltar Mazabar Kudu Jihar Kwara

Rahotanni na cewa, rundunar ‘yan sanda ta kama Sanata Rafiu Ibrahim mai wakiltar mazabar Kwara ta Kudu a jihar Kwara,

An dai kama Sanatan ne, biyo bayan wani rikici da ya barke a garin Ojuku na mazabar Kwara ta Kudu, wanda ya sa jam’iyyar APC tada jijiyoyin wuya tare da bukatar rundunar ‘yan sanda ta kama shi a matsayin silar barkewar rikicin.

Akalla mutane biyu ne aka kashe a wajen rikicin, yayin da mutane da dama su ka jikkata, rikicin da jam’iyyar PDP da APC ke zargin juna game da barkewar rikicin.

Shugaban kungiyar matasan jam’iyyar PDP na mazabar Kwara ta Kudu Muideen Abdulrahman, ya ce hakan alama ce ta cewa rundunar ‘yan sanda ta na taka rawar kidan jam’iyyar APC.

Mai Magana da yawun Sanata Bukola Sarakai, Olu Onemola, ya nuna rashin gamsuwa da matakin da rundunar ‘yan sandan ta dauka.

Ya ce kama sanatan alama ce karara da ke nuna cewa gwamnatin APC ba ta dauki demokaradiyyar Nijeriya bakin komai ba, kuma ta na amfani da rundunar ‘yan sanda domin cimma muradin ta na siyasa.