Hukumar Zabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce ya zuwa ranar rufe karbar katin zabe, ‘yan Nijeriya miliyan 72 da dubu dari 775 da dari 565 ne su ka karbi katin zaben su a hannu.
Hakan kuwa, ya yi nuni da cewa jimillar kuri’un da za a jefa a ranar Asabar mai zuwa ba za su wuce miliyan 72 da dubu dari 775 da dari 585 ba.
Hukumar ta cigaba da cewa, babu wanda za a amince ya jefa kuri’a sai wanda ya yanki katin rajistar yin zabe, ta na mai cewa yawan katunan zaben da ba a karba ba sun kai miliyan 11,228,582.
Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce katunan zabe na mutane miliyan 84 da su ka yi rajitar zabe ke hannun su a yanzu.
Ya
ce duk katunan zaben da ba a karba ba an adana su a Babban Bankin Nijeriya,
CBN, sai bayan an kammala zabe sannan hukumar za ta karbo su ta cigaba da raba
wa masu su.