Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Jagoran Mabiya Darikar Tijjaniyya
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Jagoran Mabiya Darikar Tijjaniyya

Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran mabiya Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi tir da dabi’un wasu malaman addini da ke tsine wa musulmai a kan bambancin siyasa.

Dahiru Bauchi ya nuna rashin jin dadin sa ne, yayin da Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara ya kai masa ziyara a gidan sa.

Malamin ya kuma yi jan kunne game da mahimmancin zaman lafiya da sauran al’ummar da ake zaune tare, musamman wadanda ba addinin su daya ba, ya na mai yin kira da a kara yin nesa da ra’ayin-rikau da kuma kullatar juna.

A karshe Malamin ya yi kira ga musamman al’ummar jihar Bauchi, su guji siyasar raba kawunan mabiya addinai.

Leave a Reply