Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta fitar da adadin yawan mutanen da su ka yi rijistar zabe da wadanda su ka karbi katin su zuwa yanzu.
Ta ce mutane miliyan tamanin da hudu da dubu hudu da tamanin da hudu ne su ka yi rijista a fadin Nijeriya, yayin da mutane miliyan saba’in da biyu da dubu dari bakwai da saba’in da biyar da dari biyar da biyu suka karbi katunan su.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin ta na Twitter, hukumar zaben ta ce mutane miliyan goma sha daya da dari biyu da ashirin da takwas da dari biyar da tamanin da biyu ba su karbi nasu katin ba.
A jerin yawan masu rijistar na jihohin da hukumar ta fitar, jihar Legas ce ta fi kowace jiha yawan wadanda su ka yi rijista, da mutane miliyan shida da dubu dari biyar da saba’in, da dari biyu da casa’in da daya, amma mutane miliyan biyar da dubu dari biyar da talatin da daya da dari uku da tamanin da daya ne su ka karbi katin su zuwa yanzu.
Jihar Kano ce ta biyu a wajen yawan masu rijista, inda ta ke da mutane miliyan biyar da dudu dari hudu da hamsin da bakwai, da dari bakwai da arba’in da bakwai, kuma mutane miliyan 4,696,747 ne su ka karbi katin su zuwa yanzu.