Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman, ya nesanta kan sa daga adadin mutanen da aka ce an kashe a harin da aka kai Gidan Maro da ke Karamar Hukumar Kajuru.

Ya ce ‘yan sanda na ci-gaba da bincike, kuma ba za su ambaci adadin da aka kashe ba har sai sun kammala binciken su.

A sanarwar farko da gwamna El-Rufai ya yi a ranar 15 Ga watan Fabrairu dai, ya ce mutane 66 aka kashe a cikin rugage daban-daban na Fulani, sannan bayan wani taron sirri da shugaba Muhammadu Buhari, El-Rufai ya ce wadanda aka kashen sun karu zuwa 130.

Da ya ke tsokaci game da lamarin, Sanata Shehu Sani ya ce wadanda aka kashe ba su wuce mutane 10 zuwa 15 ba.

Yayin da manema labarai su ka nemi karin bayani game da ainihin adadin mutanen da aka kashe, Kwamishinan bai jaddada adadin da aka kashe ba, amma ya ce wancan adadin da aka sanar ba daga bakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna  ya fito ba.

Kwamishinan ya kara da cewa, har yanzu jami’an sa na kan bincike, don haka ba zai iya tantance adadin da aka kashe ba sai sun kammala aikin su.