Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar PDP
Atiku Abubakar, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya na kitsa shirin amfani da Hukumar Zabe da nufin dage zabe a jihohin Borno, da Adamawa da kuma Kaduna.

A cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na Atiku Phrank Shaibu ya fitar, ya ce an kulla tuggun dage zaben a jihohin uku ne, yayin wani taron sirri da shugaba Buhari ya yi da gwamnonin jihohin uku a Abuja.

Atiku ya kuma yi gargadin cewa, duk wani yunkuri domin a haifar da tsaikon zabe a wasu jihohi ba za a amince da shi ba.

Ya ce idan har aka dage zaben a jihohin uku, hakan zai ba gwamnatin APC damar yin magudi idan ranar da za a sake yin zaben a jihohin ta zo.

Sai dai kakakin yada labarai na hukumar zabe ya ce bai san da wannan zancen ba, saboda hukumar ba ta halarci taron ba.

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus, ya ce kara wa’adin ranakun zaben wani tuggu ne da Shugaba Buhari ya kulla da nufin tabbata a kan kujerar mulki, duk kuwa da cewa ‘yan Nijeriya sun gaji da shi.

Leave a Reply