Janar Tukur Buratai, Shugaban Rundunar Sojin Kasa
Janar Tukur Buratai, Shugaban Rundunar Sojin Kasa

Shugaban rundunar sojin kasa Janar Tukur Buratai, ya maida martani a kan wata sanarwa da Atiku Abubakar ya fitar, game da umurtar sojoji su bijire wa umurnin shugaba Buhari na daukar matakin kisa a kan barayin akwatin zabe.

Buratai ya ce, sanarwar Atiku abin takaici ce, kasancewar ya taba rike babban mukami a gwamnatin Nijeriya, kuma ya san cewa rundunar soji da duk jami’an tsaro su na bin umurnin babban kwamandan rundunar sojin kasar ba tare da neman ba’asi ko turjiya ba, don haka ya ce za su bi umurnin shugaba Buhari ba tare da wata tankiya ba.

Don haka Janar Buratai ya bukaci Atiku Abubakar ya janye wannan sanarwa, tare da ba rundunar hakuri a kan yunkurin sa na dakatar da ita daga bin umurnin da dokar kasar ta tanadar mata.

Buratai ya kuma gargadi ‘yan siyasa da magoya bayan su, su kaurace wa shiga hurumin karfin ikon rundunar soji, ya na mai cewa duk wanda rundunar ta kama za su dauki mataki bisa umurnin da shugaba Buhari ya ba su.