Uwar jam’iyyar APC ta fara shawo kan zababbun gwamnonin ta da jiga-jigan jam’iyyar domin tabbatar da shugabannin majalisun tarayya sun kasance masu biyayya.
Wata majiya ta ce, ‘yan jam’iyyar APC a majalisun biyu, ciki har da sabbin ‘yan majalisa su na kokarin neman mafita gabannin rantsar da zababbun ‘yan majalisar dokoki na tarayya.
Majiyar ta ce an shawarci zababbun gwamnonin jam’iyyar APC su yi aiki tare da sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na jihohin su domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a majalisun tarayya.
An tattaro cewa yunkurin ya biyo bayan wani makirci da Shugaban majalisar dattawa mai barin gado, Bukola Saraki ke yi, na son yin kutun-kutun wajen zabar sabon Shugaban majalisar a lokacin da za a rantsar da majalisar dattawa ta tara a watan Yunin wannan shekarar.
Majiyar ta kara ta cewa, bangaren Sanata Bukola Saraki sun gana a gidan sa da ke Maitama a Abuja, inda sanatocin PDP 35 su ka amince su hada kai domin fitar da sabon Shugaban majalisar dattawa tare da maye gurbin mataimakin Shugaban majalisar dattawa.