Tsohon dan majalisar dattawa na mazabar Kano ta tsakiya Sanata Rufa’i Sani Hanga, ya bayyana irin abin da ya auku a zaben gwamna da aka maimaita a jihar Kano.
Sanata Rufa’i Hanga wanda ya wakilici jam’iyyar PDP a karamar hukumar Madobi, ya ce an yi amfani da jami’an tsaro wajen tarwatsa masu kada kuri’a a rumfunan zabe.
Ya ce wani Kwamishina a gwamnatin Ganduje ya je da wasu ‘yan sanda, inda aka rika fatattakar masu shirin kada kuri’a sannan aka yi awon gaba da kayan zaben da aka kai.
Sanatan ya cigaba da cewa, an kuma kori jami’an hukumar zaben da su ka je sa-ido a Mazabar kafin-agoro da ke cikin Garin Madobi.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sanatan ya ce wasu ‘yan daba sun rika dangwale takardun kada kuri’a a madadin jama’a, sannan an harbe wasu motocin ‘yan jam’iyyar adawa a yankin.