Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas, ta kama wasu ma’aikatan asibitin Trinity Clinic da ke unguwar Meiran da ke Legas, bisa zargin saida jaririn wata mata bayan sun yaudare ta cewa jaririn bai zo da rai ba.

Rahotanni sun ce ma’aikatan asibitin da su ka hada da wata Marbel Onochel da Dorcas Omitogun, sun saida wa wata mata mai suna Helen Okoh jaririn a kan kudi Naira 350,000.

Marbel da Dorcas dai sun bayyana wa iyayen jaririn cewa, tuni sun birne jaririn saboda kawar masu da tunanin rasa dan jaririn su.

Bayan gudanar da bincike a ofishin ‘yan sanda, Marbel da Dorcas sun ce lallai sun saida wa Mrs Okoh jaririn, inda Marbel ta dauki Naira 250,000, ta ba Dorcas Naira 100,000.

Yayin binciken, wadda ta sayi jaririn Mrs Okoh ta bayyana wa hukuma cewa, ta na matukar bukatar haihuwa ne, amma ba ta samu ba saboda ta na fama da cutar kabar mahaifa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Bala Elkana, ya ce an kwato jaririn daga hannun matar, an kuma kama wadda ta sayi jaririn tare da ma’aikatan asibitin, kuma za su gurfana a gaban kotu.