Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa shugaba Muhammadu Buhari kashedi a kan tafarkin da ya kamata ya bi na tsare-tsaren gwamnatin sa a wa’adi na biyu.
Tinubu ya shawarci shugaba Buhari ya jajirce wajen dabbaka tsare-tsaren inganta jin dadin jama’a domin ciyar da Nijeriya gaba kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zaben sa karo na biyu.
Bola Tinubu ya bayyana haka ne, a wajen bikin murnar cikar sa shekaru 67 a duniya, wanda ya gudana a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja, inda ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri da gwamnati ke yi ya kasance ya na da manufar fidda Nijeriya zuwa tudun mun tsira.
Haka kuma, Tinubu ya yi kashedin cewa, yunkurin gwamnati na kara kudin haraji ba zai haifar da komai ba face radadin talauci akan al’umma.



































