Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta sha alwashin yi wa jami’an ta garambawul, ta hanyar kara wa wasu mukamai da kuma rage ma wasu mukamai domin maido da martabar ta a idon mutane.

Rahotanni sun nuna cewa, hukumar ta kammala yanke shawara a kan ragewa wasu daga cikin jami’an ta mukamai, wadanda aka ba mukami ba tare da bin yadda doka ta tsara ba, yayin da za ta kara wa wasu girma, musamman wadanda lokacin karin girman su ya yi amma ba a kara masu ba. Sai dai wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, tuni wasu daga cikin jami’an da ake sa ran za a rage wa mukami sun garzaya kotu, domin ta dakatar da yunkurin hukumar na rage masu mukamai.

Leave a Reply