Majalisar malamai ta jihar Kano, ta bayyana zaben gwamnan jihar da aka sake a matsayin fashin damokradiyya.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya ce majalisar malamai ta Kano ta yi Allah-wadai, tare da yin watsi da fashin damokradiyya da mutanen Kano su ka fuskanta da sunan zaben gwamna.
Kofar Mata ya bayyana cewa, masu kula da zabe da dama na gida da wajen Nijeriya sun yi korafin cewa, zaben, wanda ya kamata ya zama na gaskiya da amana da kuma zaman lafiya ya zamo cike da karya doka.
Majalisar malaman ta kuma koka a kan matsalolin da su ka shafi sayen kuri’u da yaduwar rikici, wanda wasu batagari su ka dauki nauyi domin razanarwa da kuma tozarta masu zabe da jami’an jam’iyyun adawa.
Haka kuma, majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa, su yi kokarin kwato wa mutane ‘yancin su domin tabbatar da damokradiyya a Nijeriya.



































