Rahotannin sun nuna cewa, gwamnatin jihar Rivers ta bada umurnin haramta wa al’umma gudanar da zanga-zanga a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Emma Okah ya fitar, ya ce gwamnatin jihar ta ce dokar haramta zanga-zangar za ta fara aiki nan take.
Sanarwar, ta kuma bukaci dukkan jami’an tsaro su tabbatar da dokar ta yi aiki a kan kowa, domin tsaron jama’a da kawo kwanciyar hankali.
Mista Okah ya shaida wa manema labarai cewa, zanga-zanga ta na kara yawaita a jihar, kuma da yawan sun shafi zaben da aka kammala.
Rahotanni sun bayyana cewa, an samu barkewar rikice-rikice har da kisan kai yayin zabubbukan jihar da aka gudanar makonnin da su ka gabata.,ߴY���



































