Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shugabannin kungiyar kiristoci ta Nijeriya tabbacin barin Nijeriya fiye da yadda ya same ta a shekara ta 2015.

Yayin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar a karkashin  jagorancin Reberan Samson Ayokunle, shugaba Buhari ya bada tabbacin cewa, gwamnatin sa za ta cigaba da magance muhimman kalubalen da Nijeriya ke fuskanta, musamman harkar tsaro da tattalin arziki da cin hanci da rashawa.

Kungiyar dai ta ziyarci fadar shugaban kasa ne domin taya shugaba Buhari murnar samun nasarar lashe zabe.

Da ya ke bayyana ra’ayin sa a kan rawar da kungiyoyin addini su ka taka a shekaru hudun da ya yi ya na mulki, Buhari ya sha alwashin ci-gaba da nuna goyon bayan shirye-shiryen da kungiyar addini ke gabatarwa, mai dauke da manufar kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin kai a Nijeriya.

Leave a Reply