Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ba zababben gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP shahadar lashe zaben da ya yi.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris ne aka kammala zaben gwamnan jihar Adamawa, inda dan takarar jam’iyyar PDP Ahmadu Fintiri ya kada gwamna mai ci Mohammed Bindow na jam’iyyar APC.
Jam’iyyar PDP ta samu nasara ne da kuri’u dubu 376 da 552, yayin da jam’iyyar APC ta zo ta biyu da kuri’u dubu 336 da 386.
Kwamishinan Zabe na jihar Adamawa Farfesa Andrew Haruna ne ya kaddamar da Amadu Fintiri a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben.



































