Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta kama dan majalisar wakilai na mazabar  Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin, dangane da harin da aka kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar Rabi’u Kwankwaso.

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne magoya bayan dan majalisar su ka kai wa ayarin Kwankwaso hari, bayan sun yi wa wata hanyar shiga kauyen Kofa kawanya tare da yunkurin hana mutane shiga kauyen.

Akalla mutane biyar aka kashe, yayin da wasu da dama su ka ji rauni lokacin da bangarorin biyu su ka yi arangama da juna, an kuma kona gidan dan majalisar, yayin da aka kona motoci sama da 10 kurmus.

Mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda Danbature da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Mohammed Wakili, sun ziyarci wajen da lamarin ya faru, sannan su ka bada umurnin a kama dan majalisar.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, tuni aka garzaya da majalisar zuwa helkwatar rundunar da ke Bompai a cikin birnin Kano domin amsa tambayoyi.

Leave a Reply