Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta ce jami’an ‘yan sanda ke da hakkin kula da rumfunan zabe ba sojoji ba.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, yayin da ya ke bayani a kan shirin zabe da kuma amsa tambayoyi a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja.
Ya ce tsarin da aka sani shi ne, ba hakkin sojoji ba ne kula da tsaro a rumfunan zabe, amma ya danganta da gayyatar da su ka samu daga jami’an ‘yan sanda.
Farfesan
ya kara da cewa, hukumar zabe ta na aiki ne da hukumar ‘yan sanda, amma idan su
na fuskantar wata barazana su na iya gayyato sauran jami’an tsaro da su ka hada
da sojoji domin su taimaka.