Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce an karbi belin dan majalisar wakilai Abdulmumin Jibrin, da ta gayyata sakamakon samun wani rikici.

Jami’in hudda da jama’a na rundunar DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da haka.

‘Yan sanda dai sun gayyaci dan majalisar ne da ke wakiltar mazabr Kiru da Babeji a majalisar wakilai tare da wasu ‘yan siyasa kan zargin haddasa rikici.

An zargi Abdulmimin da sauran ‘yan siyasar ne da laifin hana wata tawaga wuce wa, dalilin da ya haifar tashin hankali da rasa rayuka.

Daga cikin wadanda ‘yan sanda suka kama har da shugaban karamar hukumar Babeji.

Rundunar ‘yan sandan ta ce za ta ci gaba da bincike bayan da ta ba da belin Abdulmumin Jibrin.

Leave a Reply