Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa INEC
Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa INEC

Shugaban hukumar ta zabe ta kasa INEC Farfesa Muhmud Yakubu ya ce akalla ‘yan Nijeriyar miliyan 11 da dubu 228 da dari 582 ba za su samu damar karbar katunan zaben su na din-din-din ba, har zuwa lokacin da hukumar ta rufe karba.

Farfesa Mahmood Yakubu ya ce kashi 86 da digo 63 cikin 100 na adadin masu rijistar zaben a Nijeriya ne kadai suka karbi katunan zaben su, lamarin da ke nuna cewa akwai kashi 13 da digo 37 da suka gaza karbar katinan na su.

Hukumar INEC ta ce, adadin ‘yan Nijeriya da suka yi rijistar zaben ya kai mutane miliyan 84 da dubu 4 da 84, yayin da miliyan 11 da dubu 228 da dari 582 su ka ga za karbar katun na su, matakin da ke nuna cewa mutane miliyan 72 da dubu 775 da dari 502 ne kadai suka cancanci kada kuri’a a zabukan da ake gudanarwa a wannan rana.

Hukumar ta kara da cewa, jihohin Lagos da Kano da Ogun, su ne kan gaba wajen yawan mutanen da basu karbi katunan zaben su ba, inda ta ce a jihar Lagos kadai akwai adadin mutane miliyan 1 da dubu 38 da dari 902 da basu karbi katin ba.

Leave a Reply