Ellen Johnson Sirleaf, Tsohuwar Shugabar Liberia Jagorar Tawagar Ta ECOWAS
Ellen Johnson Sirleaf, Tsohuwar Shugabar Liberia Jagorar Tawagar Ta ECOWAS

Tawagar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS da ke sa ido a zaben Najeriya ta ce ta yaba da tsarin hukumar INEC na gudanar da zaben shugaban kasa.

Cikin wata sanarwa, jagorar tawagar ta ECOWAS tsohuwar shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, ta ce tun dage zaben a makon da ya gabata sun sa ido sosai ga ayyukan hukumar INEC musamman kalubalen da ta fuskanta na raba kayan zabe.

Ta ce ta yi farin cikin ganin yadda aka tunkari matsalar ta hanyar aiki tukuru don magance ta domin samar da yanayi mai inganci dan gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ta jinjinawa ‘yan Najeriya kan yadda suka yi hakuri da kalubalen da suka fuskanta yayin da aka dage zaben sa’o’i kadan a bude rumfunan zabe.

A halin da ake ciki da ‘yan Najeriya sun kada kuri’a zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da ‘yan majalisar dattawa da na wakilai.

ECOWAS ta yi kira ga ‘yan Najeriya su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda har zuwa lokacin da aka sanar da sakamakon zaben.

Leave a Reply