Shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce za a yi amfani da dokokin zabe ne wajen hukunta wadanda su ka aikata laifuffuka yayin gudanar da zaben shekara ta 2019.

Farfesa Yakubu ya bayyana haka ne, a wajen taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a babban dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, shugaba Muhammadu Buhari ya ce duk wanda ya saci akwatin zabe ya sani hakan a bakin ran sa ya ke.

Yayin da ya ke tsokaci game da kalaman na shugaban kasa, Farfesa Yakubu ya ce za a hukunta wadanda su ka saci akwatin zabe ne bisa tanadin dokar zabe.

Ya ce matsayar hukumar zaben shi ne, za ta yi amfani da dokar zabe wajen hukunta duk wadanda aka samu da hannu wajen aikata laifuffuka yayin zabe.

Leave a Reply