Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya cewa, kada su karaya sakamakon dage zaben da akayi, ya na mai bukatar kowa ya fito domin kada kuri’a su a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.
Buhari ya kuma nemi afuwar ‘yan Nijeriya sakamakon matsalolin da su ka fuskanta a sanadiyar dage zaben da aka yi, ya na mai yaba masu bisa juriya da hakurin da su ka yi, inda ya sha alwashin ganin an gudanar da zaben gaskiya da adalci a fadin Nijeriya.
Idan dai ba a manta ba, a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu ne, hukumar zabe ta dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokoki da na tarayya.
Wani
dan majalisar tarayyar kasar Amurka Chris Smith, ya ce babu wani mai laifi
sakamakon dage zaben da ya wuce shugaba Buhari da makarraban sa, inda ya bukaci
gwamnatin kasar Amurka ta sa ido a kan sha’anin Nijeriya.