Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata rahoton da ke cewa, ya na kokarin ganin wasu ‘yan takara da ya ke goyon baya sun lashe zaben da aka sake ta kowane hali.
Shugaba Buhari, ya bayyana haka ne a wani sako da ya fitar ta hannun mai magana da yawun sa Malam Garba Shehu.
Buhari, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa, ya na tilastawa al’umma a kan su zabi wasu ‘yan takara, inda ya kara da cewa, sam babu kamshin gaskiya a kan wannan batu, saboda haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su rika zaben duk wadanda su ke so a lokacin zabe.
Shugaban
kasa ya mika godiyar sa ga ‘yan Najeriya
kan yadda suka sake zabar sa a karo na biyu.