Tsohon Gwamnan jihar Kano Kuma madugun Kwankwasiyya Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayan Kwankwasiyya su cire jar hula har sai bayan zabe,
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata tattaunawar sa da wani gidan radiyo mai zaman kansa a Jihar Kano, inda ya ce tun daga Juma’a kowa ya cire jar Hula sai bayan zabe.
Sai dai kuma al’umma sun fara tambayar ko mene ne dalilin da ya sa Kwankwaso ya ba mabiyan nasa wannan Umarni.
A tattaunawar da aka yi da wasu magoya bayan tafiyar Kwankwasiyyar, sun bayyana cewa sun samu labari Gwamnatin Jihar Kano ta dauko wasu matasa tare da raba masu makamai da jajayen huluna domin tada hargitsi a wuraren zaben.
An tuntubi wasu makusantan Gwamnatin Jihar Kano domin jin gaskiyar wannan zargi na ‘yan Kwankwasiyya, Safiyanu Ibrahim Tafidan Gwagwarwa, ya bayyana mana cewar batun shaci fadi ne kawai.
Ya ce Gwamnatin
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnati ce mai tarbiyya kuma bata da wani shirin
daukar wasu matasa domin yin wani abu mara kyau, ya ce su da suke da kyakkyawan
zaton Nasara a wurin Allah me zai su yin wani da abu da zai rage kimar
Gwamnati.