Bayanan da ke fito wa daga jihar Kano sun nuna cewa, jami’an tsaro sun dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa komai ya tafi daidai a guraren da aka kusa samun tangarda a yayin gudanar da zabukan cike gurbi na jihar da aka gudanar a Asabar dinnan.
Tun da fari dai an samu rahotannin da ke nuni da cewa, a wasu daga cikin mazabun an so a samu hargitsi sakamakon zafin da bangarori biyu na manyan jam’iyyun jihar da ke fafatawa, watau APC da PDP, su ka dauka.
Wasu rahotanni sun ce, jami’an tsaro sun kama kwamishinan ayyuka na musamman Muntari Ishak Yaksai, da dan majalisar dokokin jihar Baffa Babba Dan’Agundi, amma daga bisani rundunar ‘yan sanda ta karyata rahoton.
Bugu da kari, an samu hargitsi a wasu wurare, to amma mafi yawan runfunar zaben, an gudanar da komai lafiya ba tare da samun tashin-tashina ba.
A tattaunawarsa da manema labarai, mukaddashin shugaban ‘yan sanda na kasa mai kula da zaben na Kano, DIG Antony Micheal Ogbizi, ya ce, a Gama da ke karamar hukumar Nassarawa, an samu fitowar jama’a sosai kuma zaben ya tafi lafiya kalau.
Ya ce a ‘yan kalilan
wasu wuraren da a ka samu sa’insa sun shiga tsakani, don dawo da zaman lafiya,
ya kara da cewa, ba su samu rahoton kawo ‘yan daba a zaben ba, inda ya ce sun
zuba isassun ‘yan sanda, Jita-jitar cewa
an kama wasu kwamishinoni karya ce tsagwaron ta.