Rahotannin da muka samu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun bankawa kayan zabe wuta, a gundumar Azendeshi da ke garin Chito, jihar Binuwe.
Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye kayayyakin zaben ne a wata makarantar firamare ta gwamnati, kafin wasu ‘yan ta’adda da ke aiki karkashin wata jam’iyyar siyasa suka fi karfin jami’an tsaro tare da bankawa kayan zaben wuta.
An kuma samu makamancin wannan rahoton a wani yanki na karamar hukumar Kwande, inda wasu ‘yan ta’adda suka ci zarafin wani jami’in INEC tare da lalata kayan zabe, amma dai rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.