Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bukaci ‘Yan Najeriya Da Su Yi Fitan Farin Dango Domin Kada Kuri’a A Zaben Gwamnonin Da Na ‘Yan Majalisun Jihohi Da Zai Gudana A Wannan Makon.

Shugaban Ya Kuma Bukaci Masu Kada Kuri’a Da Su Natsar Da Kawunan Su Tare Da Bin Dokiki Da Hukumomi Suka Shirya A Lokacin Gudanar Da Zabubbukan.

Ya Ce Akwai Hukunce-Hukunce Masu Tsanani Da Za A Dauka Akan Wadanda Aka Samu Da Laifuffukan Da Suka Shafi Satar Akwati, Magudin Zabe, Ta Da Hatsaniya Da Sauran Su.

Shugaba Buhari Ya Ce Jami’an Tsaro Za Su Ci Gaba Da Aikin Tsaron Lafiya Da Dukiyoyin Al’umma Tare Da Tabbatar Da Cewa An Basu Damar Zaben Abin Da Suke So.

Sannan Ya Shawarci ‘Yan Najeriya Da Su Kara Ba ‘Ya’yan Jam’iyyar Apc Dama, Domin Shawo Kan Matsaloli Da Ingnata Rayuwar Al’umma Kamar Yadda Aka Saba.

Ya Kuma Shawarci Matasa Da Kada Su Bari ‘Yan Siyasa Marasa Kishin Kasa Su Rika Amfani Dasu Domin Cimma Wata Bukata Tasu Ta Daban.