Siyasar Kano na ci gaba jan hankali, sakamakon girman hamayyar dake tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu da ke kokarin lashe kujerar gwamna.

Zaben ya fi jan hankali ne tsakanin jam’iyya mai mulki ta APC a jihar da kuma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Tun kafin a fara tattara sakamakon kananan hukumomi wani bangare na siyasar ta Kano ya fara murnar nasarar lashe zabe, wani abin da ake gani zai haifar da rudani a jihar.

Kano da ke da yawan kananan hukumomi 44, Sakamakon wani yanki na birnin Kano ba shi ne zai tabbatar da wanda ya ci zaben gwamna ba, sai idan an kammala tattara dukkanin sakamakon na kananan hukumomi.

Rahotanni sun ce ko wasu kananan hukumomi da ke cikin kwaryar birnin Kanon inda ake murna babu wadda ta bayyana cewa ta kammala tattara sakamakon zaben na gwamnoni har ace an kai ga bayyana sakamakon.

Sun ce za a iya samun tsaikun samun sakamakon wasu kananan hukumomi saboda rashin hanya mai kyau musamman irin su Doguwa, da Tudun Wada, da Rogo, da Kiru, da kuma Tsanyawa.

Akwai manyan kananan hukumomi masu mazabu 14 zuwa 13 wasu 10, inda za a iya daukar lokaci kafin tattara sakamakon zaben na gwamna.