Mansur Muhammad Dan-Ali , Minister Of Defence
Mansur Muhammad Dan-Ali , Minister Of Defence

Duk da barazanar Maharan da su ka addabi al’ummar jihar Zamfara, bai hana jama’ar jihar fitowa domin zaben gwamnoni da ’yan majalisar dokoki na jihar ba.

 Al’ummar jihar Zamfara dai sun fito sun cika runfunan zabe, don zabar wadanda su ke so a matakin gwamna da ‘yan majalisar dokokin jiha.

Ministan Tsaro Birgediya Mansur Dan Ali, ya yaba da yadda jama’a su ka fito rumfunan zabe cikin kwanciyar hankali da lumana babu wata hatsaniya.

Da ya koma kan batun tsaron jihar, ministan ya tababtar wa al’ummar jihar Zamfaran bukatar ganin an samar da filin girgin sama na sojin sama a tsakanin Birnin Magaji da Zurmi, don ganin bayan ‘yan ta’addan da su ka addabi yankin.

Shima mataimakin gwamnan jihar Zamfara bayan kammala kada kuri’ar sa ya bayyana wa manema labarai cewa dole a jinjina wa jami’an tsaro ganin yadda su ka samar da tsaro a fadin rumfunan zabe.

Wani dan gudun hijira da ke zaune a karamar hukumar Maradun Bello Mai-Jama’a, ya bayyana wa manema labarai cewa, fatan su ga wanda ya samu nasara a gwamna shi ne ya taimaka wajen maida su garuruwan su kuma ya dawo da tsaro a fadin kauyukan jihar baki daya.