A halin da ake ciki an fara kidayar kuri’un da aka kada a zaben Gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi, inda zaben Gwamnonin ya gudana a jihohi 29, na ‘yan majalisun kuma a jihohi 36 na fadin Najeriya.

A mafi akasarin sassan Najeriyar dai, zabukan sun gudana ne cikin kwanciyar hankali, sai dai a wasu bangarorin, an dan fuskanci matsalolin yiwa masu kada kuri’a da jami’an zabe barazana.

Gamayyar kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya da ke sa ido kan zabukan sun bayyana rahotannin mutuwar mutane 7 kan zabukan na ranar Asabar.

Jihohin da aka fi fuskantar matsalolin rikici, tare da hasarar rayuka sun hada da Bayelsa da Ebonyi da kuma Legas.

A Bayelsa da Ebonyi, rahotanni sun ce an samu hasarar rayukan mutane 2 a kowace jiha, yayinda a Legas aka kone ababen ahawa akalla 35 tare da kashe mutane 2 a wasu sassan jihar, kamar yadda jami’an sa ido kan zabukan suka tabbatar.

A Rivers kuwa, tsohon gwamnan jihar kuma ministan sufuri a yanzu, Rotimi Amechi ya ce mutane 3 sun rasa rayukan su a rikicin zabe.

A bangare guda kuma, kakakin hukumar zaben Najeriya na jihar Rivers, ya shaidawa kamfanin daillancin labarai na AFP cewa wasu tsageru sun yi garkuwa da jami’an su, sai dai bai bayyana adadin su ba.