Wata Kotun tarayya da ke Abuja, ta sauya matsayar ta a kan hukuncin da ta yanke na dakatar da tattara sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, inda yanzu haka ta amince a cigaba da tattara sakamakon zaben.

A baya dai kotun ta saurari karar da dan takarar jam’iyyar APC Gwamna Mohammed Abubakar ya shigar, inda ya bukaci a dakatar da hukumar zabe tattara sakamakon zaben.

Sai dai Alkalin kotun ya yi watsi da batun lauyan dan takarar Ahmed Raji, wannda ya bukaci a dakatar da tattara sakamakon zaben Tafawa Balewa.

A hukunci da alkalin ya yanke a baya, Inyan Ekwo ya ba bangarorin biyu umarnin tsayawa yadda su ke har sai kotun ta yanke hukunci.

Alkalin ya ce, karar da aka shigar a gaban kotu kara ce da ta danganci zabe, kuma kotun sauraren kararrakin zabe kadai ce za ta iya yanke hukunci a kan wannan lamari.

Tun farko Lauyan dan takarar APC ya ce, kotun sauraren kararrakin zabe ta na sauraren kara ne kawai bayan an bayyana sakamakon zabe, a cewar sa karar da ya shigar a yanzu ta kunshi abubuwa ne da su ka faru kafin a bayyana sakamakon zabe.