Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karbi rahoton kwamitin bada shawara a kan yadda za a fara biyan sabon karin albashi da majalisa ta amince da shi.

Kwamitin dai, ya mika wa shugaba Buhari rahoton ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 9 watan Janairu ne shugaba Buhari ya kafa kwamitin a karkashin jagorancin masanin tattalin arziki Bismarck Rewane, bayan jaddada aniyar sa ta kara ma fi karancin albashin ma’aikata.

Shugaba Buhari, ya fara bayyana niyyar sa ta yin karin albashin ne a watan Disamba na shekara ta 2018, yayin gabatar da kasafin kudi a gaban ‘yan majalisun dokoki na tarayya.

Ya ce kwamitin zai ba gwamnati shawarwari a kan yadda za ta samu sukunin biyan mafi karancin albashin ba tare da an samu hauhawar farashin kayayyakin masarufi da matsalar rage yawan ma’aikata ba. Sai dai ministan kasafi da tsare-tsare Udo Udoma, ya ce gwamnatin tarayya za ta kara yawan kudin haraji a kan kayan masarufi domin samun kudaden da za ta iya biyan sabon karin albashin.