Gobara ta lakume azuzuwa bakwai a makarantar sakandare ta Badawa da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Kakakin rundunae ‘yan sanda na jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba a rasa rayuka a gobarar ba.

An dai danganta lamarin ne da wutar lantarki, wadda ta tashi daga dakin gwaje-gwaje na makarantar, kuma gobarar ta fara ne da misalin karfe 1:30 na dare.