Hukumar zabe mai zaman kanta INEC za ta soke jam’iyyun siyasan da ba su tabuka abin a zo a gani ba a zaben da ya gabata tare da kuma nazari akan yadda jam’iyyun siyasan da suka shiga zaben da aka gudanar suka kashe kudade da kuma hanyoyin da suka bi wajen samun kudaden.

Festus Okoye, Shugaban Kwamitin Yada Labarai Da Wayar da Kan Masu Zabe Na INEC
Festus Okoye, Shugaban Kwamitin Yada Labarai Da Wayar da Kan Masu Zabe Na INEC

Shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Festus Okoye, ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, ya ce hukumar za ta shiga wannan aikin ne da za ran an kammala dukkannni zabukkan dake kasa da kuma shari’o’in da suka shafi zaben da aka gudanar.

Okoye, ya ce, hukumar INEC na amfani da hanya na musamman wajen bin diddigin yadda jam’iyyu suka kashe kudaden yakin neman zabe, sannan kuma za a  sake tsarin yadda jam’iyyu ke kashe kudade bayan an kammala harkokin zaben gaba daya.

Ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda wasu manyan ‘yan Nijeriya ke kokarin kawo wa shirin hukumar INEC na gudanar da sahihi zabe a Najeriya cikas.

Okoye, ya kuma bayyana cewa, na da kyakkyawan ra’ayin cewa, lokacin magudin zabe ya wuce, lokacin da mutum zai shiga daki ya rubuta abinda yake so da nufin sakamakon zabe ya zama tarihi.