Mohammed Buba Marwa, Shugaban Kwamitin Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi
Mohammed Buba Marwa, Shugaban Kwamitin Yaki Da Shan Miyagun Kwayoyi

Shugaban kwamitin yaki da shan miyagun kwayoyi, Buba Marwa, ya ce bincike ya nuna cewa daga cikin ‘yan Nijeriya miliyan 180, miliyan 15 daga cikinsu ‘yan kwaya ne.

Marwa, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Legas ya ce, lamarin abin tayar da hankali ne a kididigar da kungiyoyin duniya suka yi, wanda ya nuna cewa kashi 15 na mutanen dake mu’amala da kwayoyi a Najeriya suke.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana haka ne a wani taro da kwamintinsa suka yi da jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a Katsina.

Ya ce Najeriya na fustankar babbar barazana a halin yanzu akan abin daya shafi shan miyagun kwayoyi, amma gwamnatin tarayya ta samar da kwamitin ne domin fito da hanyoyin maganin matsalar shan miyagun kwayoyi.

Tsohon gwamnan jihar Legas Buba Marwa, ya bayyana wa Gwamna Aminu Bello Masari cewa, kwamitin na su ya fara aiki ne tun a watan Disamba na shekarar da ta gabata, amma babban abinda suka sa a gaba shi ne dakile yadda ake shigo da kwayoyi Najeriya.