Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai Farouk Adamu Aliyu, ya cewa jam’iyyarsu ta APC ta koyi darasi dangane da yadda aka gudanar da zabubbukan a Najeriya.

Adamu Aliyu, ya bayyana hakan ne  a lokacin da yake hira da kafar yada labarai ta BBC,  ya ce dauki dora ko kuma kakaba ‘yan takara na daya daga cikin abubuwan da suka kawo ma jam’iyyar tasgaro a wasu jihohi wanda hakan ya yi sanadiyar rasa wasu kujerun gwamnoni da ma na ‘yan majalisa.

Ya bada misali da jihar Ogun inda ya bayyana cewa gwamnan ya yi ungulu da kan zabo, inda gwamnan jihar dan APC ne amma ya jagoranci wata jam’iyya domin ganin cewa an kada jam’iyyar APC a zaben gwamna.

Ya kuma ba da misali da jihohin Imo da Bauchi da kuma Adamawa inda ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida ne suka yi sanadiyar faduwar jam’iyyar zabe a jihohin.

Ya yi kira ga jam’iyyar APC cewa a shekarar 2023 ta tabbatar an yi zaben fitar da gwani na jam’iyyar sahihi kuma ingantacce a fadin kasar nan.

Leave a Reply