Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kafa wani kwamiti da zai binciki wasu gwamnoni da akai zarginsu da cin hanci da rashawa da za ran wa’adin mulkinsu ya kare.

Akalla jihohi 12 ne za su samu sabbin gwamnoni a ranar 29 ga watan Mayu, bayan karewar wa’adin gwamnonin da ke ci a yanzu, jihohin sun hada da Lagos, Ogun, Oyo, Imo, Kwara, Nasarawa, Yobe,  Borno,  Adamawa, Bauchi, Gombe, Zamfara.

Daga cikin gwamnoni 12,  guda hudu daga cikinsu ana zarginsu da cin hanci da rashawa, gwamnonin sun hada da Rochas Okorocha na jihar Imo; da gwamnan Kwara, Abdulfatah Ahmed; da shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari; da gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun.

Okorocha, wanda jam’iyyar APC ta dakatar da shi, ana zarginsa da karkatar da naira billiyan 1,  shi kuma gwamnan jihar Zamfara Yari EFCC na binciken sa da karkatar da naira milliyan 500 mda kuma  da milliyan dari 5 na Paris Club.

Gwamna Ahmed na jihar Kwara kuwa, zai gurfana ne gaban EFCC bisa zargin karkatar da naira billiyan 1 mako daya kafin zaben shugaban kasa,  shi kuwa gwamna Ibikunle Amosun na jihar  Ogun hukumar EFCC na zarginsa da karkatar da naira billiyan 4 karkashin shirin bayar da rance ga manoma na ‘Anchor Borrowers’ da gwamnatin tarayya ta turawa manoman jihar.

Leave a Reply