Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, za ta rufe dukkan hanyoyin shigowa Nijeriya ta kasa daga karfe 12 na ranar Juma’a zuwa karfe 12 na ranar Lahadi, 24 ga watan Fabrairu na shekara ta 2019.
A cikin wata sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida Janar Abdulrahman Dambazau ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin takaita shige da fice a kan iyakokin Nijeriya a ranakun zabe.
Kamar yadda ya ke cikin sakon da Kwantrolla Janar na hukumar shige da fice ta kasa Muhammad Babandede ya raba wa manema labarai, ya ce saboda zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, Ministan harkokin cikin gida ya bada umurnin rufe dukkan iyakokin kasa daga karfe 12 na ranar Juma’a zuwa karfe 12 na ranar Lahadi.
Ya ce za a dauki matakin ne, domin takaita shige da fice a kan iyakokin Nijeriya a ranakun zabe, don haka ana sanar da al’umma su lura da wannan umurnin kuma su tabbatar sun yi biyaya gare shi.