Farfesa yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Vice President Yemi Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa yemi Osinbajo, ya karyata rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga kujerar sa saboda  wani sabani da ya samu da shugaba Muhammadu Buhari.

An dai samu jita-jitan cewa Osinbajo ya nuna bacin ran sa a kan rashin gayyatar sa ganawar da shugaba Buhari ya yi da jami’an tsaro da gwamnonin Nijeriya a  Abuja

Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Doyin Okupe, ya ce an hana Osinbajo shiga dakin taron, ya na mai cewa Osinbajo ya ce ba a sanar da shi a kan ganawar ba, kuma lokacin da ya samu labari an hana shi shiga.

Sai dai Farfesa Yemi Osinajo ya karyata wannan labari, inda ya ce labarin bogi na yawo musamman a wannan lokaci da ‘yan Nijeriya ke kokarin zabe, don haka ya ce bai yi murabus ba.

Osinbajo ya kara da cewa, ya na kan aikin sa na bautar ‘yan Nijeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.