Duk da cewa jihar Kogi na daya daga cikin jihohi bakwai da ba a gudanar da zaben gwamna ba, saboda wa’adin mulkin gwamnonin su bai cika ba, hakan bai hana masu kada kuri’a fitowa, don zaben ’yan majalisar dokokin jiha ba.

Masu jefa kuri’a sun yi fitar farin dango tunda sanyin safiya, don kada kuri’arsu ga ’yan takarar da su ka kwanta mu su a rai.

A yayin da a ka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana a wasu rumfunan zaben, wasu rumfunan kuma an samu tirka-tirka.

Rahotanni daga sassa daban-daban na jihar sun yi nuni da cewa an gudanar da zabukan na majalisun dokokin lami lafiya sai dai dan abinda ba a rasa ba na tashin hankali a wasu wuraren.

Jihar Kogi mai kananan hukumomi 21 na da kujerun ’yan majalisun dokoki 25 kuma ’yan takara da su ka fito daga jam’iyyu daban-daban ne su ke fafatawa a zaben.

A na dai dakon samun dukkan sakamakon zabukan na majalisun dokoki a jihar Kogi a gobe Litinin.

Leave a Reply