Rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta tabbatar da harbe wani dan majalisar wakilai na tarayya a Ibadan babban birnin jihar.

Wasu mutane ne da ba a san ko su wanene ba suka harbi dan majalisar a wata rumfar zabe a karamar hukumar Lagelu cikin garin Ibadan.

Rahotanni sun ce ya mutu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan bayan mummunan raunin da ya samu daga harbin da aka yi masa a kai zuwa ido.

Babu dai wani karin bayani daga ‘yan sanda ko an kama wadanda suka harbi dan majalisar mai suna Olatoye Temitope Sugar.

Leave a Reply