Rahotanni sunce al’ummar hausawa mazauna jihar Legas sune suka mamaye runfunar kada kuri’u a wasu yankuna da ke fadin jihar sakamakon yadda al’ummar yarbawa suka zauna a gida duk da cewa sun mallaki katin zabe.
Kididdiga ta nuna cewa, Jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan mutanen da suka karbi katin zabe amma akasarin su sun karbi katin ne saboda wasu manufofi daban ba kada kuri’a ba.
Kididdigar hukumar zabe mai zaman kanata INEC ta nuna cewa, mutanen Legas miliyan 5 da dubu 500 ne suka karbi katin zaben, amma yawan wadanda suka kada kuri’un su a zaben shugaban kasa bai wuce miliyan 1.
Sai dai Hukumar ta INEC
ta ce, duk da karancin fitowar masu kada kuri’ar a Legas, ta gamsu da yanayin
cinkoson jama’a a rumfunan zabe a wannan karon idan aka kwatanta da zaben
shugaban kasa da aka yi makawanni biyu da suka gabata.